Hukunce-Hukuncen Kiran Sallah a Musulunci
-
Upload
tarbiyyarmusulunci -
Category
Documents
-
view
188 -
download
21
Transcript of Hukunce-Hukuncen Kiran Sallah a Musulunci
Hukunce-Hukuncen Kiran Sallah
A
Musulunci
Ahmad Bello Dogarawa
Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria [email protected]
A Matsayin Takarda Da Aka Gabatar Wajen Taron Qara Wa Juna Sani,
Da Kwamitin Da’awah Da Kula Da Harkokin Masallatai Na Jihar Kaduna
Ya Shirya Wa Limamai Da Ladanai Da Sauran Masu Da’awah,
A Makaratar Sakandare ta Alhuda-Huda, Zaria
2006
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 1 6/12/2010
1.0 GABATARWA
Wannan qasida za ta yi tsokaci ne a kan ‘Hukunce-hukuncen Kiran Salla a
cikin Qur’ani da Sunnah bisa fahimtar Magabata na Qwarai’. Qasidar za
ta tattauna a kan ma’anar kiran salla da falalarsa da hukunce-hukuncen da
ke rataye da shi. Daga qarshe, qasidar za ta yi tsokaci a kan waxansu kura-
kurai da suka shafi kiran salla.
Ina roqon Allah Ya yi mana muwafaqa.
2.0 MA’ANA DA HUKUNCIN KIRAN SALLA ( )
Kalmar (Kiran Salla) na da ma’ana a harshen larabci ( ) da ma’ana a
Shari’ah. A harshen larabci, kalmar na nufin ‘sanar da wani abu’ (
). Kalmar ta zo da irin wannan ma’ana a cikin faxin Allah ( ):
3 , da faxin Allah ( ): 27 , da faxin
Allah ( ): 109
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 2 6/12/2010
A Shari’ah, kalmar na nufin ‘sanar da lokacin Sallah da lafuzza sanannu,
kevantattu da Sharia’h ta tabbatar’. Kuma ana kiransa sabo da mai
kiran Sallah na kiran mutane zuwa ga yin salla ne. Irin wannan ma’ana ta
zo cikin faxin Allah ( ):
58 da faxinSa:
9
Malamai sun yi ittifaqi a kan shar’ancin kiran salla, amma sun yi savani
game da hukuncinsa. Magana mafi qarfi ita ce: kiran salla farilla ce ta
kifaya ( ) a kan maza, ga kowace sallar farilla, a halin tafiya da
zaman gida, a yanayin zafi ko sanyi. Haka nan ma, kiran salla farilla ce ta
kifaya ga sallar Juma’a.
Daga cikin dalilan da ke tabbatar da farlancin kiran salla, akwai:
1. Lazimtar kiran salla da aka yi tun daga lokacin da aka shar’anta shi
har zuwa rasuwar Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare
shi) ba tare da sakaci ko rangwame ba.
2. Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya sanya kiran
salla a matsayin alama ta Musulunci da ke nuna mutanen gari sun
shiga Musulunci kuma suna riqo da shi. Hadisi ya tabbata daga Anas
bn Malik (Allah Ya yarda da shi)
3. Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi umurni da
kiran salla. A cikin Hadisin Malik bn al-Huwairith (Allah Ya yarda
da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
Haka nan, Anas bn Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
A cikin Hadisin Abdullah bn Zaid (Allah Ya yarda da shi), Manzon
Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
1 Bukhari da Muslim
2 Abu Dawud, Tirmidhi da Ibn Majah
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 3 6/12/2010
Haka nan, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce
wa Uthmaan bn Abil ‘Aas (Allah Ya yarda da shi):
Bayan wannan, Manzon Allah (SAW) y ace:
Wannan ya sa Shaykhul Islam Ibn Taimiyyah (Allah Ya jiqansa) ya ce:
2962264
Wajibcin kiran salla a kan maza ne ban da mata. Kiran sallar mace ga
maza bai inganta ba. Amma idan mata suka kira salla a tsakaninsu da
murya qasa-qasa ta yadda maza ba za su ji ba, an so haka, kuma kiran
sallar ya yi.5 An tambayi Abdullah bn Umar (Allah Ya yarda da shi): ‘mata
za su kira salla (a tsakaninsu)?’ Sai ya fusata, ya ce: ‘Zan hana zikirin
Allah ne?’6 Haka nan, an tambayi Anas bn Malik (Allah Ya yarda da shi):
‘wajibi ne mata su kira salla?’ Ya ce: ‘A’a, amma idan sun yi (a
tsakaninsu), zikirin Allah ne.’7
An yi savani game da shekarar da aka shar’anta kiran salla. Ibn Hajar
(Allah Ya jiqansa) ya rinjayar da shekara ta farko bayan Hijira.8
3. FALALAR KIRAN SALLA DA MASU KIRAN SALLA
Babu shakka, kiran salla na daga manya-manyan alamomi na addinin
Musulunci, kuma kasancewarsa abu muhimmi, kiran salla da masu kiran
salla na da falala mai yawa da suka tabbata a cikin sahihiyar Sunnar
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi). Daga cikin falalar
akwai:
1. Masu kiran salla su ne mafi tsawon wuya a ranar qiyama. Manzon
Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
3 Abu Dawud, Nasa’i, Tirmidhi da Ibn Majah
4 Abu dawud da Ahmad: Isnadin Hadisin na da xan rauni
5 Maganar da aka ruwaito daga Abdullah bn Umar (Allah Ya yarda da shi) cewa: ‚Babu kiran salla da
iqama da juma’a da wankan juma’a a kan mata‛, bai inganta ba. Baihaqi ya ruwaito shi da isnadi mai
rauni 6 Ibn Abi Shaybah da isnadi hasanun
7 Ibn Abi Shaybah da isnadi sahihi
8 Fathul Baari, 2/78
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 4 6/12/2010
2. Kiran salla na koron shaixan, ya sanya shi gudu. Manzon Allah (tsira
da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
3. Da mutane sun san alherin da ke cikin kiran salla, da sai an yi quri’a
kafin a fitar da wanda zai kiran salla. Manzon Allah (tsira da aminci
su tabbata a gare shi) ya ce:
4. Duk halittar da ta ji kiran salla, za ta yi wa mai kiran sallar shaida
ranar qiyama. Abu Sa’eed al-Khudri (Allah Ya yarda da shi) ya ji
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
5. Ana gafarta wa mai kiran salla gwargwadon nisan muryarsa.
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
6. Ana gafarta zunuban mai kiran salla kuma a shigar da shi Aljanna.
Uqubatu bn `Aamir (Allah Y a yarda da shi) ya ji Manzon Allah
(tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
7. Annabi (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi addu’ar neman
gafara ga masu kiran salla. Ya ce:
9 Muslim
10 Bukhari da Muslim
11 Bukhari da Muslim
12 Bukhari
13 Nasa’i da Ahmad
14 Abu Dawud da Nasa’i
15 Abu Dawud da Tirmidhi
A qarqashin wannan Hadisin waxansu Malamai sun fahimci cewa kiran salla ya fi limanci falala
domin kuwa amana ta fi lamuni, kuma gafara ta fi shiriya. Dangane da Manzon Allah (tsira da aminci
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 5 6/12/2010
4. SHARUXXAN KIRAN SALLA DA SIFFOFIN MAI KIRAN
SALLA
Kiran salla na da sharuxxa kamar haka:
Shigan lokacin salla: sabo da Hadisin Manzon Allah (SAW):
Amma sallar Asuba ana yin kiran
kafin alfijir ya fito.
Niyya, kasancewar dukan ayyuka sai da niyya, kamar yadda Hadisi ya
nuna
Amfani da larabci wajen kiran salla, kasancewar shi ne ya tabbata.
Kuma ya kasance bisa adadin da Hadisai ingantattu suka tabbatar, ba
tare da qari ko ragi a cikin lafazi ko adadi ba
Rashin kura-kurai da ke canza ma’ana da tsarin larabci
Yin kiran salla bai xaya ba tare da yankewa ba
Jeranta kalmomi da lafuzzan kiran salla tun daga farko har zuwa qarshe
Xaga murya, ta yadda ba wanda ke kiran salla ne kawai zai ji ba.
Manzon Allah (SAW) ya ce:
Dangane da mai kiran salla, wajibi ne ya zamanto adali kuma amintacce,
mai kiyaye lokaci. Allah ( ) Ya ce: . Manzon
Allah (SAW) ya ce: Mutumin da ba adali ba
ne, ba a amince masa tun da ya sava wa wannan Hadisi. Ibn Taimiyyah
(Allah Ya jiqansa) ya ce:
su tabbata a gare shi) da Halifofinsa (Allah Ya yarda da su) kuwa, Malamai sun ce: sun yi limanci ne
maimakon kiran salla sabo da wajibi ne a kansu, kuma quncin lokaci ba zai ba su damar haxa kiran
salla da limanci ba, kuma ayyukan da suka shafi maslahar al’umma da ke kansu sun fi kiran salla
muhimmanci.
16
Bukhari da Muslim 17
Bukhari 18
57
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 6 6/12/2010
Shaykh Muhammad bn Saalih al-`Uthaymeen (Allah Ya jiqansa) ya
bayyana cewa kalmar adalci ta qunshi kasancewar mai kiran salla ya
zamanto: Musulmi, mai hankali, namiji, shi kaxai, adali, mumayyazi.19
Bayan wannan, an so mai kiran salla ya yi wannan aiki don neman lada da
dacewa da yardar Allah, ba tare da an ba shi wani abu ba. Manzon Allah
(SAW) ya ce wa Uthmaan bn Abil `Aas (RA): .
Amma idan aka rasa wanda zai yi ba tare da an biya shi ba, ko kuma ya
zamanto mutane sun ga maslaha cikin biyansa albashi, babu laifi ya
karva.21
An so mai kiran salla ya zamanto mai murya sosai, sabo da Manzon Allah
(SAW) ya ce wa Abdullah bn Zaid (RA): , kamar yadda aka so ya zamanto mai daddaxar murya.
Haka nan, an fi son mai kiran salla ya kasance yana iya gane shigan lokaci
da kansa. Idan bai sani ba, babu laifi matuqar akwai wani amintacce da zai
riqa sanar da shi shigan lokaci, domin Ibn Ummi Maktum (RA), xaya daga
cikin masu kiran salla a masallacin Manzon Allah (SAW) makaho ne, ba
ya kiran salla har sai an sanar da shi lokaci ya yi.23
5. SIFFAR KIRAN SALLA
Bincike da bin diddigi cikin ingantattun Hadisai na Manzon Allah (SAW)
na tabbatar da siffofin kiran salla guda uku. Siffofin kiran salla da suka
tabbata su ne:
Siffa ta farko (Jumloli goma sha biyar): Siffar ta qunshi yin kabbara guda
huxu a farko, sa’an nan sauran jumlolin sau bibbiyu, ban da jumlar qarshe,
kamar yadda Hadisin Abdullah bn Zaid (RA) ya tabbatar
19
262 20
Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa’i da Ibn Majah 21
2702132244 22
Abu Dawud da Ibn Majah 23
Bukhari da Muslim 24
Abu Dawud, Tirmidhi da Ibn Majah
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 7 6/12/2010
Siffa ta biyu (Jumloli goma sha bakwai): Siffar ta qunshi yin kabbara guda
biyu a farko, sa’an nan a maimaita kalmomin shahada da murya ma fi
xaukaka a kan ta farko. Sauran jumlolin kuma sau bibbiyu, ban da jumlar
qarshe, kamar yadda Hadisin Abu Mahdhurah (RA) ya tabbatar
Siffa ta uku (Jumloli goma sha tara): Siffar ta qunshi yin kabbara guda
huxu a farko, sa’an nan a maimaita kalmomin shahada da murya ma fi
xaukaka a kan ta farko. Sauran jumlolin kuma sau bibbiyu, ban da jumlar
qarshe, kamar yadda Hadisin Abu Mahdhurah (RA) a wata ruwayar ya
tabbatar
Abubuwan lura:
1. Dukan waxannan siffofi sun inganta, don haka kowace siffar aka
xauka, babu matsala. Sai dai kuma idan aka riqa nau’antawa, ta
yadda za a yi wannan a wani lokaci, wani lokacin kuma a yi waccan,
to ya fi.
2. Sallar Asuba ta kevanta da kira sau biyu: kafin alfijir ya fito da kuma
bayan alfijir ya fito, kamar yadda ta kevanta da qarin
bayan sau biyu. An so a tsakanin kiran salla
na farko da na biyu ya zamanto ba tazara sosai. Hujjar kiran salla na
farko kafin alfijir ya fito na cikin Hadisin Abdullah bn Mas’ud (RA),
Manzon Allah (SAW) ya ce:
25
Muslim 26
Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa’i da Ibn Majah 27
Bukhari da Muslim
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 8 6/12/2010
3. Malamai sun yi savani game da kiran sallar da ake faxin
a ciki. Waxansu Malamai na ganin a cikin kira na biyu ake faxi.
Amma Magana ma fi qarfi ita ce: ana faxinsa ne a kiran salla na
farko don faxakar da wanda ke ibada cikin dare ko wanda zai yi
azumi cewa alfijir ya kusa fitowa, kuma a farkar da mai barci don ya
yi shirin sallar Asuba, kamar yadda Hadisi ya nuna.
4. Yin amfani da kiran salla da aka xauka a cikin kaset ko wata na’ura
xaukar sauti maimakon haqiqanin kira da mai kiran salla zai yi ga
kowace sallar farilla, bai inganta ba. Sanannen abu ne cewa kiran
salla ibada ce, don haka dole ne ta zamanto [ ]
5. Idan aka haxa salloli guda biyu a lokaci xaya, kamar haxa sallar
Zuhr da Asr a filin Arafah ko Magrib da Isha’ a Muzdalifah ko aka
haxa salloli guda biyu sabo da ruwa, ko sabo da wni dalili da ya
tabbata a Shari’ah, za a yi kiran salla ne ga ta farko kuma a yi iqama
ga kowacensu. A cikin Hadisin Jabir bn Abdillah (Allah Ya yarda da
shi) dangane da haxa sallar Zuhr da Asr a Arafah da Manzon Allah
(tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi:
Dangane da haxa sallar Magrib da Isha’ kuwa, Jabir (Allah Ya yarda
da shi) ya ce:
6. An so wanda ya kira salla ya zamanto shi ne zai yi iqama, kamar
yadda Bilal (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana yi. Kuma ba a
fara yin iqama ko mutane su miqe tsaye har sai an hango liman yana
zuwa, ko kuma ya miqe idan yana cikin masallacin ne. Wannan shi
ne abin da ya tabbata a cikin Sunnah. Hadisi ya tabbata cewa
Idan wani ya kira salla, wani kuma ya yi iqama, ba bu laifi. Hadisin
da ke cewa da Hadisin da ke nuna cewa Abdullah bn
Zaid (RA) ke yin iqama bayan Bilal (RA) ya kira salla, bas u inganta
ba. Sabo da haka ba za a iya dogaro da su a cikin wannan mas’ala
ba.31
28
Muslim 29
Muslim 30
Muslim 31
Akwai nau’o’in iqama guda biyu da suka tabbata a cikin Sunnah. Nau’in farko ya qunshi jumala
goma sha xaya, kamar yadda yake cikin Hadisin Abdullah bn Zaid (RA):
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 9 6/12/2010
6. LADUBBAN KIRAN SALLA
Akwai ladubban da ake buqatar mai kiran salla ya kiyaye. Daga cikin
ladubban akwai:
1. Alwalla a lokacin da za a kira salla, sabo da dalilan da ke nuna
karhancin ambaton Allah ba tare da alwala ba. Hadisi ya tabbata
cewa an yi wa Manzon Allah (SAW) sallama, alhali yana alwala,
amma bai amsa sallamar ba har sai bayan ya kammala. Sa’an nan ya
ce:
Idan mutum ya kira salla alhali ba shi da alwala, dukan Malamai na
ganin kiran sallar ya yi. Amma idan ya kira salla alhali yana cikin
janaba, da yawa daga Malamai na ganin rashin ingancin wannan
kira. Sai dai kuma Magana ma fi qarfi ita ce kiran sallar ya yi,
kasancewar ba bu wani dalili sahihi da ya hana hakan.
2. An so a kira salla a tsaye, matuqar ba bu wata larura da za ta hana
hakan. Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: 33
3. Fuskantar alqibla, kasancewar mala’ikan da Abdullah bn Zaid (RA)
ya gani a cikin mafarki, ya kira sallar ne a tsaye, yana mai fuskantar
alqibla.34
4. Shigar da yatsu a cikin kunnuwa yayin kiran salla ko da mai kiran
salla na amfani da na’urar xaukaka sauti, sabo da Hadisin Abu
Juhaifah (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
Nau’i na biyu na cikin Hadisin Abu Mahdhurah (RA), kuma ya qunshi jumloli goma sha bakwai
kamar haka:
32 Abu Dawud, Nasa’i da Ibn Majah
33 Bukhari da Muslim
34 Duba littafin 232 na Shaikh Muhammad Naasiruddeen al-Albaanee
35 Tirmidhi da Ahmad
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 10 6/12/2010
5. Juyawa vangaren dama lokacin faxin , da juyawa
vangaren hagu yayin faxin sabo da Hadisin Abu Juhaifah
(RA) ya ce:
6. An so a kira salla a farkon lokaci, sabo da Hadisin Jaabir bn
Samurah (Allah Ya yarda da shi):
37
7. Haxa tsakanin duk kabbarbari guda biyu, sabo da Hadisin Umar bn
al-Khattab (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (tsira da
aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
7. LADUBBAN MAI SAURAREN KIRAN SALLA
Mustahabbi ne ga wanda ya ji kiran salla ko iqama ya maimaita abin da
mai kiran salla ko wanda ke tayar da iqama ke faxi har da jumlar
in ban da wurin jumlolin da ake son ya ce
sabo da Hadisin Umar bn al-Khattab (RA), Manzon Allah
(tsira da aminci su tabbata a gare shi), ya ce:
Idan mai kiran salla ya kammala kalmomin shahada, an so mai sauraro ya
ce:
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: 36
Abu Dawud 37
Ibn Majah da Ahmad 38
Muslim 39
Muslim
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 11 6/12/2010
Idan mai saurare ya kammala maimata abin da mai kiran salla ya faxi,
kamar yadda ya gabata, an so ya yi salati ga Manzon Allah (tsira da aminci
su tabbata a gare shi), sa’an nan ya nema wa Manzon Allah (tsira da
aminci su tabbata a gare shi) wasila ta hanyar karanta addu’ar da ta tabbata
a cikin Sunnah. Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
Dangane da addu’ar nema wa Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a
gare shi) wasila, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya
ce:
Daga nan sai ya yi wa kansa addu’a, yana mai neman falalar Allah da
biyan buqatunsa na duniya da lahira. Manzon Allah (tsira da aminci su
tabbata a gare shi) ya ce:
An so wanda ya saurari kiran salla ya yi waxannan abubuwa gaba xaya,
kasancewar ba wani vangare da ya kore wani a cikinsu.
Bayan wannan, an haramta wa wanda salla ta wajaba a kansa ya fita daga
masallaci bayan an kira salla ba tare da wani uzuri ba (kamar yin alwala ko
wanka ko kuma rashin lafiya), sai dai idan yana da niyyar dawo wa kafin a
fara sallar. Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) ya ga wani mutum ya fita
daga masallaci bayan an kira salla, sai ya ce:
8. KURA-KURAI DA AKE YI A CIKIN KIRAN SALLA
Lura da yadda ake kiran salla a masallatai da dama, da yadda masu sauraro
ke maimaita kalmomin da ake faxi na nuna cewa akwai kura-kurai da
40
Muslim 41
Muslim 42
Ahmad da Abu Dawud. Lafazin Abu Dawud shi ne: 43
Muslim
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 12 6/12/2010
dama da ake aikata wurin kiran sallar. Daga cikin irin waxannan kura-
kurai, akwai:
1. Xaukar cewa kiran salla Sunnah ne ba farilla ta kifaya ba. Bayanai da
dalilan da ke nuna wajibcin kiran salla sun gabata. Wannan ya sa
Shaykhul Islam Ibn Taimiyyah (Allah Ya jiqansa) ya ce:
2. Rarrabe kabbarbari ta yadda za a xan dakata bayan kowace kabbara
xaya, maimakon a haxa kabbarori guda biyu, wato mai kiran salla ya
ce daga nan ya numfasa, sa’an nan ya ce ya qara
numfasawa, sa’an nan ya ce ya qara numfasawa, sa’an nan ya
ce . Yin amfani da wannan salo a wajen kiran salla ya sava wa
zahirin Hadisin Umar bn al-Khattab (RA). A cikin Hadisin, Manzon
Allah (SAW) ya haxa tsakanin kabbarbari guda biyu, sa’an nan ya
xan yi shiru.
3. Shigar da harafin alhamza da ke nuna tambaya ko neman sani (
) a cikin lafazin , ta yadda kalmar za ta zamanto .
Faxin haka zai mayar da ma’anar kalmar ta koma wato shin
Allah Mai girma ne?
4. Qara harafin alif ( ) bayan harafin ba’un ( ) a lafazin ta yadda
zai zamanto . Yin haka kuskure ne babba kuma canza ma’anar
kalmar ce, domin kuwa jam’i ne na , wato ganga. Kenan,
kamar mai kiran salla na siffanta Allah Maxaukakin sarki ne da
wannan siffa.
5. Musanya harafin da a cikin lafazin ta yadda lafazin zai koma
ko kuma qara a tsakanin da , ta yadda lafazin zai
koma
44
226545
Muslim
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 13 6/12/2010
6. Kyakkyarma murya da jan lafuzzan kiran salla fiye da qima da rera
shi kamar waqa ( ). Kuskure ne mai kiran salla ya ce
maimakon . Da yawa daga Malamai sun ce irin
wannan jan haruffa fiye da qima, bidi’a ce.
7. Cire harafin wajen ta yadda zai zamanto
8. Juyar da harafin ya koma wurin , ta yadda za a kira
lafazin da . Hakan sai ya canza ma’anar ta koma ku yi
gaggawa zuwa ga falalen dutse maimakon ku yi gaggawa zuwa ga babban rabo
9. Wuce qa’ida da qetare xabi’a wurin yin maddah ( ) ga harafin da
ke cikin lafazin . Hakan sai ya sanya lafazin ya zamanto
10. Shafe harafin da yin shadda ( ) ga harafin cikin lafazin
. Hakan sai ya sanya lafazin ya koma
11. Wuce qa’ida da qetare xabi’a wurin yin maddah ( ) ga harafin da
ke cikin lafazin , ta yadda zai koma
12. Qara harafin cikin lafazin , ta yadda zai koma
maimakon
13. Wuce qa’ida da qetare xabi’a wurin yin maddah ( ) ga da ke
cikin jumlar , ta yadda zai koma
14. Qara harafin bayan da ke cikin lafazin , ta yadda zai koma
15. Qara harafin bayan da ke cikin lafazin , ta yadda zai koma
Hukunce-hukuncen Kiran Salla a Musulunci, Ahmad Bello Dogarawa, Page 14 6/12/2010
16. Qara jumlar da jumlar a cikin addu’ar nema
wa Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) wasila
bayan an kammala kiran salla. Wannan qari bai zo ba sai a cikin
Hadisai masu rauni, kamar yadda Ibn Hajar ya tabbatar a cikin
littafin
17. Faxin bayan mai kiran salla ya ce ko kuma .
Abin da ya tabbata a cikin Sunnah shi ne a maimaita waxannan
lafuzza, kamar yadda bayani ya gabata. Haka nan ma, kuskure ne
faxin idan mai yin iqama ya ce .
Hadisin da ya zo da wannan lafazi yana da tsananin rauni, kamar
yadda Malamai suka tabbatar. Don haka, sai a maimaita abin da mai
yin iqama ya ce, bisa la’akari da Hadisin da ya zo da maganar
maimaita abin da mai kiran salla ya faxi.
18. Shafa idanuwa da manyan yatsu a lokacin da mai kiran salla ya faxi
kalmomin shahada . Hadisin da ya yi
magana a kan haka na qarya ne ( ), kamar yadda manyan
Malamai suka tabbatar.
9. GODIYA DA KAMMALAWA
Daga qarshe, ina godiya ga kwamitin Da’awah da al’amuran Masallatai na
jihar Kaduna, da ya ba ni damar gabatar da wannan qasida, a matsayin
gudummuwa ta ga limamai da masu kiran salla na wannan jiha.
Abin da ya ke daidai, daga Allah ne, kuma ina roqon Ya ba mu lada, kuma
Ya ba mu ikon aiki da shi. Kuskuren da ke ciki, daga gare ni ne, kuma
daga shaixan; Allah da ManzonSa sun
barranta daga gare shi. Ina roqon Allah Ya yafe mani, kuma Ya ba ni ikon
fahimtarsa, don in gyara.